logo

HAUSA

Shugaban Rasha ya sa hannu kan takardar amincewa da baiwa shugaban CMG lambar karramawa ta abota

2021-11-19 15:17:58 CRI

Shugaban Rasha ya sa hannu kan takardar amincewa da baiwa shugaban CMG lambar karramawa ta abota_fororder_211119-Saminu 3-Shen Haixiong1

A jiya Alhamis 18 ga wata ne shafin yanar gizo na ofishin shari’ar kasar Rasha dake Moscow, ya fitar da wata sanarwa mai kunshe da dokar shugaban kasa, wadda ta bayyana amincewar shugaba Vladimir Putin, da baiwa shugaban gungun kamfanonin watsa labarai na kasar Sin CMG Mr. Shen Haixiong lambar karramawa ta abota.

Shugaban Rasha ya sa hannu kan takardar amincewa da baiwa shugaban CMG lambar karramawa ta abota_fororder_211119-Saminu 3-Shen Haixiong

Dokar shugaban kasar ta bayyana cewa, Shen Haixiong ya cancanci wannan lambar yabo ne, bisa gudummawarsa ga kara dinkewar abokantaka, da hadin gwiwa tsakanin al’ummun Sin da na Rasha, da inganta fahimtar juna tsakanin su.

A bana ne ake cika shekaru 20 da kulla yarjejeniyar kyakkyawar makwaftaka, da kawance, da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu. Hakan kuma na zuwa a gabar da shugabannin kasashen 2, ke kara dora muhimmanci ga musaya, da hadin gwiwa ga ayyukan raya bil adama tsakanin al’ummun kasashen biyu.  (Saminu)