logo

HAUSA

Martin Jacques: Ya kamata tsarin demokradiyya ya kunshi ra’ayin duniya baki daya ba wata kasa guda ba

2021-11-19 14:46:46 CRI

Martin Jacques: Ya kamata tsarin demokradiyya ya kunshi ra’ayin duniya baki daya ba wata kasa guda ba_fororder_211119-Faeza 3-Martin

Martin Jacques, malami kuma mai fashin baki kan harkokin siyasa, ya ce dole ne batun demokradiyya ya zama ra’ayin duk duniya ba wata kasa guda ba, a wannan zamani na wayewar kai da sauyin yanayi. Yana mai cewa, mayar da hankali kan duniya baki daya, abu ne mai matukar muhimmanci.

Da yake jawabi a wani taro ta kafar intanet kan demokradiyya da ’yancin bil adama, wanda ofishin kasar Sin da na Rasha dake ofishin MDD dake Geneva suka shirya, Martin Jacques, ya ce kasar Sin ba ta bin tsarin wata kasa, shi ya sa shawararta ta gina al’umma mai makoma ta bai daya ga dukkan bil adama ta zama wani sabon tunani game da duniya da ma demokradiyya.

Ya ce sashen yammacin duniya ya damu da ko daidaikun kasashe na bin mahangarsa na tsarin demokradiyya, amma bai damu da ko tsarin kasa da kasa na bisa tafarkin demokradiyya ba, kuma ba zai dore a wannan sabon zamani na wayewar kai ba. (Fa’iza Mustapha)