logo

HAUSA

Yaro Bai San Wuta Ba Sai Ya Taka

2021-11-17 21:05:21 CRI

Yaro Bai San Wuta Ba Sai Ya Taka_fororder_微信图片_20211117162817

BY CRI HAUSA

A kwanakin baya ne, sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya bayyana a yayin wata hira da aka yi da shi cewa, wai kasarsa na da kudurin tabbatar da cewa, yankin Taiwan zai iya kare kansa. Sai dai kuma Anthony Blinken, ya manta cewa, ya bayyana a wani taron manyan jami’an kasashen Sin da Amurka da aka gudanar a karshen watan Oktoba, cewa "Amurka za ta ci gaba da martaba manufar Sin daya tak a duniya". Don haka, ta yaya mutumin da ke furta irin wadannan kalamai na kwan-gaba-kwan baya, ya dace da zama babban jami'in diflomasiyyar Amurka?

Ya kamata Antony Blinken da ma sauran jami’an Amurka su fahimci cewa, yanzu haka akwai kasashe 180 a duniya, wadanda suka amince tare da goyon bayan manufar kasar Sin daya tak a duniya, kuma wannan ita ce yarjejeniya ta gaskiya da kasashen duniya suka amince da ita.

Bugu da kari, dokar nan ta dangantakar Taiwan da Amurka da Amurkar ta kirkita, ta saba alkawurran da ita kanta Amurka ta dauka a cikin sanarwoyin hadin gwiwa guda uku da Sin da Amurka suka cimma a tsakaninsu. Idan maye ya manta, to uwar diya ba ta manta ba.

A kokarin da kasar Sin ke yi na kara fahimtar da Amurka da ma kasashen duniya kan manufar kasar Sin daya tak a duniya, sanarwar da aka fitar bayan kammala cikakken zaman karo na shida na kwamitin tsakiya na JKS karo na 19, a kwanakin nan, ta bayyana karara cewa, kasar Sin za ta ci gaba da martaba ka'idar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da kuma matsaya irin daya da aka cimma a shekarar 1992, wadda ke adawa da ayyukan ’yan aware dake neman ’yancin kai na Taiwan, da tsoma baki daga waje. Wannan ya nuna a fili irin tsayin daka na kasar Sin, da kuma matsayinta na kare ikon mallakar kasa, da tsaro da moriyar ci gabanta.

Koda a yayin zantawarsa da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden ta kafar bidiyo a ranar Talata 16 ga watan Nuwamba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana matsayinsa bisa ka'ida game da batun Taiwan, inda ya jaddada aniyarsa ta yin kokarin sake hadewa da yankin cikin lumana bisa gaskiya da himma, amma idan ’yan aware masu neman ’yancin kan Taiwan suka tunzura jama’a, ko suka zarce layin da aka shata, dole ne a dauki tsauraran matakai.

A halin da ake ciki yanzu, babban yankin kasar Sin, ya amince da jagoranci da himma a dangantakar dake tsakaninsa da zirin Taiwan, kuma batun sake hadewar kasar Sin, wani yanayi ne na tarihi da ba za a iya jurewa ba. A don haka, kasar Sin tana gargadin bangaren Amurka da kada ya raina kudiri da karfin da jama'ar kasar Sin suke da shi, na kare ikon mallakar kasa da cikakkun yankanansu. Kuma duk wani mataki na kalubalantar manufar kasar Sin daya tak a duniya, da kokarin dakile kokarin sake dinkuwar kasar Sin baki daya, to hakika ba zai taba yin nasara ba. Duk tsuntsun da ya janyo ruwa, hakika shi ruwa zai doka. (Ibrahim Yaya)