logo

HAUSA

Uganda Ta Karbi Kashi Na Biyu Na Tallafin Allurar COVID-19 Da Kasar Sin Ta Samar Mata

2021-10-20 21:05:45 CRI

Talatar nan ne, kasar Uganda ta karbi kashi na biyu na tallafin allurar rigakafin cutar COVID-19 na kamfanin Sinovac da gwamnatin kasar Sin ta samar mata.

Karamar ministar kula da lafiya a matakin farko ta kasar, Margaret Muhanga ta ce, ta karbi alluran rigakafin a dakunan ajiye kayayyakin lafiya na kasa da ke Entebbe, mai nisan kilomita 40 kudu da Kampala, babban birnin kasar.

Ministar ta yaba da gudummawar, a yayin da kasarta ke kara fadada kamfen din rigakafi don ceton rayuka tare da bude harkokin tattalin arziki.

A jawabinsa Zhang Lizhong, jakadan kasar Sin a Uganda, ya ce gudummawar ta zo ne a daidai lokacin da kasashen biyu ke bikin cika shekaru 59 da kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu, kuma yana daga cikin kudirin kasar Sin na gina al'ummar duniya ta bai daya a fannin kiwon lafiya ga kowa.

Baya ga ba da gudummawar dalar Amurka miliyan 100 da kasar Sin ta baiwa shirin COVAX, kasar Sin ta kuma ta yi alkawarin ba da karin allurar rigakafin miliyan 100 ga sauran kasashe masu tasowa a wannan shekara. (Ibrahim)

Ibrahim