logo

HAUSA

Sin ta samar da babbar gudummawa da tabbatar da ra’ayin bangarori daban daban

2021-10-17 17:01:03 CRI

Sin ta samar da babbar gudummawa da tabbatar da ra’ayin bangarori daban daban_fororder_1017-1

Mataimakin babban sakataren MDD mai kula da harkokin tattalin arziki da zamantakewar al’umma Liu Zhenmin, ya bayyana a kwanakin baya cewa, a matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kana kasa ta biyu da ta fi ba da kaso mafi yawa ga MDD, da kuma matsayinta na wakiliyar dindindin a kwamitin sulhun MDD, har kullum kasar Sin tana kiyaye samar da babbar gudummawa da tabbatar da ra’ayin bangarori daban daban.

Liu Zhenmin ya bayyana cewa, yau shekaru 50 da suka gabata, babban taron MDD ya zartas da kudurin mayar da dukkan hakkin kasar Sin bisa doka a MDD. Kudurin ya maida kasar Sin ta shiga tsarin kasa da kasa bisa tushen MDD, da kafa hulda tare da kasa da kasa, wanda ya aza tubali mai kyau ga kasar Sin wajen bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima a gida. Haka zalika, kudurin ya maida tsarin MDD a matsayin tsarin dake wakiltar bangarori daban daban, da samun daidaito yayin da ake raya dangantakar dake tsakanin manyan kasashe, da kuma sa kaimi ga raya tattalin arzikin duniya bisa tsarin bai daya.

Liu Zhenmin ya kara da cewa, ya kamata kasa da kasa su kara yin hadin gwiwa da juna don cimma nasarar yaki da cutar numfashi ta COVID-19, musamman kasashe masu samun alluran rigakafin cutar su kara taimakawa kasashe masu tasowa wajen samun alluran don hana yaduwar cutar. Ya kamata kasa da kasa su kara yin hadin gwiwa da juna a kokarin cimma nasarar yaki da cutar ta COVID-19, da sa kaimi ga cimma ajandar samun bunkasuwa mai dorewa ta MDD nan da shekarar 2030 don tinkarar sabon kalubalen da zai fito a nan gaba. (Zainab)