logo

HAUSA

Sin ta samar da tallafin jin kan bil Adama ga Somalia

2021-10-17 16:54:16 CRI

Sin ta samar da tallafin jin kan bil Adama ga Somalia_fororder_索马里

A ranar Asabar kasar Sin ta bayar da gudunmawar tallafin jin kan bil Adama ga kasar Somalia, a kokarin kyautata alakar dake tsakanin kasashen biyu.

Fei Shengchao, jakadan kasar Sin a Somalia, ya bayyana cewa, tallafin jin kan bil Adaman da kasar Sin ta samar ya hada da tantunan kwana  10,000, gidajen saura 50,000, akwatin taimakon gaggawa 20,000 da injunan auna nauyin jarirai, da na’urorin auna bugun zuciya da kuma ta auna yanayin zafin jiki.

A cewar jakada Fei, gwamnatin kasar Sin ta aike da taimakon ne duk kuwa da karuwar tsadar samar da kayayyakin da na jigilarsu. Ya kara da cewa, wannan wata hanya ce da kasar Sin take taimakawa sauran kasashe.

Jakadan ya ci gaba da cewa, kasashen Sin da Somalia sun shafe tsawon lokaci suna kyautatawa junansu da kuma nuna juriya a lokutan da suke fama da wahalhalu.

Ministar ayyukan jin kai da yaki da bala’u ta kasar Somalia, Khadijo Mohamed Diriye, ta yabawa gwamnatin kasar Sin sakamakon samar da tallafin jin kan bil Adama ga kasarta, ta ce taimakon ya zo a daidai lokacin da ake matukar bukatarsa.(Ahmad)

Ahmad