logo

HAUSA

An Kammala Taron Sufuri Mai Dorewa Na MDD Karo Na Biyu A Beijing

2021-10-17 16:08:36 CRI

An Kammala Taron Sufuri Mai Dorewa Na MDD Karo Na Biyu A Beijing_fororder_sufuri

A jiya Asabar an kammala taron kasa da kasa kan sufuri mai dorewa na MDD karo na biyu, inda aka fidda sanarwar Beijing.

Domin jaddada muhimmancin tsarin sufuri mai dorewa, sanarwar ta Beijing ta jaddada alfanun gaggauta yin sauye-sauye da nufin cimma nasarar sufuri mai dorewa a matsayin wani muhimmin ginshikin da zai samar da kyakkyawar makoma ga bil Adama baki daya.

A cewar sanarwar, idan aka yi amfani da sabbin fasahohin zamani, kuma aka yi aiki da su yadda ya kamata, za su kasance a matsayin jigon da zai warware kalubaloli masu yawa dake shafar sufuri mai dorewa. Sanarwar ta kuma ba da kwarin gwiwa game da hadin gwiwar kasa da kasa, da samar da kwarewa da musayar ilmi a tsakanin kasashen duniya.

Akwai bukatar magance yanayin da ake ciki a yankunan karkara da wasu kasashen dake cikin yanayi na musamman ta hanyar fadada tsarin sufuri mai dorewa da ababen more rayuwar jama’a. Sannan ya kamata a kara kokari wajen kiyaye aukuwar haddura a hanyoyin mota, kuma a inganta tsarin kandagarkin annoba da matakan da ake dauka na kai dauki a fannin sufuri.

Mahalarta taron sun yi maraba da kafa cibiyar kirkire-kirkire da musayar ilmi ta kasa da kasa a fannin sufuri mai dorewa a kasar Sin, wacce za ta mayar da hankali wajen musayar ilmi da samar da kwarewa a kasashe masu tasowa.(Ahmad)

Ahmad