logo

HAUSA

Rahoto: Karairayin Amurka kan batun dakin gwajin Wuhan siyasa ce

2021-10-16 21:27:23 CRI

Rahoto: Karairayin Amurka kan batun dakin gwajin Wuhan siyasa ce_fororder_1271709975007592450

Shafin intanet na World Socialist ya wallafa wani sharhi a ranar Talata inda ya bayyana cewa, karairayin da Amurka ta yi game da batun dakin gwaje-gwaje na Wuhan na kasar Sin batu ne wanda bai dogara kan binciken kimiyya ba sai dai batu ne dake shafar siyasar duniya, kuma manufar wadannan karairayin an yi su ne da nufin bata sunan kasar Sin da Sinawa, da kuma danganta su da annoba wacce ta kashe Amurkawa sama da miliyan daya.

Rahoton mai taken “Karya game da dakin gwajin Wuhan: Mujallar The Washington Post ta koyawa Amurka nuna kiyayya," sharhin wanda ya soki sabon tsokacin da mujallar The Post ta yi, inda ya karyata zargin dake cewa an kirkiri kwaryar cutar COVID-19 a kasar Sin ta hanyar manyan kwararrun masana binciken kwayar cutar corona na duniya.

Sharhin ya bayyana cewa, babu wata kalma ko da guda daya a cikin sharhin wanda kwararrun masana ba su yi watsi da ita ba, da hukumomin kasa da kasa, har ma da ita kanta gwamnatin Amurka.(Ahmad)