logo

HAUSA

An zabi masanin aikin lambu na kasar Sin a matsayin "Jarumin Abinci"

2021-10-16 21:28:43 cri

An zabi masanin aikin lambu na kasar Sin a matsayin "Jarumin Abinci"_fororder_20211016173717703

Ranar 16 ga watan Oktoba ita ce ranar Abinci ta Duniya, Hukumar Abinci da Aikin Noma ta MDD (FAO) ta kaddamar da jerin bukukuwa a Rome, babban birnin kasar Italiya a ranar 15 ga wata.

A wannan shekara, FAO ta zabi mutane ko kungiyoyi 25 a matsayin "Jaruman Abinci" tare da yin kira da a inganta tsarin aikin noma. Daga cikinsu, an karrama Ye Ming’er, mataimakin farfesa a fannin aikin lambu a jami'ar Zhejiang ta kasar Sin inda aka ba shi lambar yabo na "Jarumin Abinci" sakamakon kokarin da yake na "yada fasahar 'ya'yan itatuwa har tsawon shekaru 35 ". Shafin yanar gizon FAO ya bayyana cewa, ayyukan Ye Ming'er sun nuna cewa, yin kirkire-kirkire kan fasahohin shuke-shuke na iya habaka girman amfanin gona da kara yawansu, a waje guda kuma ana iya kiyaye albarkatun halittu da kyautata zaman rayuwar manoma. (Bilkisu)