logo

HAUSA

An kammala zagayen farko na babban taron COP15 tare da share fagen tsara jadawalin kiyaye mabambantan halittu bayan shekarar 2020

2021-10-16 17:23:22 CRI

An kammala zagayen farko na babban taron COP15 tare da share fagen tsara jadawalin kiyaye mabambantan halittu bayan shekarar 2020_fororder_d50735fae6cd7b895cf73a4fa7cc07aedb330e50

A jiya Juma’a an kammala kashin farko na babban taro kan mabambantan halittu karo na 15 wato (COP15), a Kunming, babban birnin lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin, inda aka share fagen tsara jadawalin inganta kiyaye mabambantan halittu a kasa da kasa bayan shekarar 2020, yayin da ake fatan dawowa babban taron a shekarar 2022.

Jimillar wakilai 2,918 ne suka halarci taron na wannan zagaye a Kunming, yayin da wasu wakilan 2,478 suka halarta ta kafar bidiyo, kamar yadda mashirya taron suka bayyana.

Huang Runqiu, ministan muhalli na kasar Sin, kana shugaban babban taron na COP15, ya bayyana cewa, tsarin tafiyar da muhalli na duniya na fuskantar kalubaloli masu yawa da ba a taba ganin irinsu ba, kuma tilas ne kasa da kasa su yi aiki tare wajen karfafa hadin gwiwa don gina ingantaccen tsari mafi dacewa da manufar wayewar kan bil adama wajen kiyaye muhallin halittu da kyautata makomar mabambantan halittu domin cimma nasarar samar da dawwamamman cigaban duniya da kuma cigaban bil adama daga dukkan fannoni.(Ahmad)