logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun lalata haramtattun matatun mai 51 a yanki mai arzikin mai na kasar

2021-10-15 10:06:03 CMG

Sojojin Najeriya sun lalata haramtattun matatun mai 51 a yanki mai arzikin mai na kasar_fororder_211015-Najeriya-Ahmad

Dakarun sojojin Najeriya dake aiki a yankin kudancin kasar mai arzikin man fetur sun yi nasarar lalata wasu haramtattun matatun mai guda 51 a yakin da suke yi da masu yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa da sauran ayyukan bata gari, kakakin hukumar sojojin kasar ya bayyana hakan.

Da yake jawani a taron manema labarai a Abuja game da ayyukan da sojojin ke gudanarwa a fadin kasar, Benard Onyeuko, kakakin hukumar sojojin ya ce, dakarun sojojin dake aiki a rundunar Operation Delta Safe daga jahohin kudancin kasar da suka hada da Rivers, Abia, Cross River, Bayelsa, Akwa Ibom da Imo ne suka gudanar da ayyukan.

Onyeuko ya fadawa ‘yan jaridu cewa, sojojin suna cigaba da gudanar da ayyukansu a shiyyar kudu maso kudancin kasar domin fatattakar masu yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa da sauran masu aikata muggan laifuka.

Ana yawan samun ayyukan bata masu barnata bututan mai da masu satar albarkatun man a kasar mafi arzikin mai a Afrika, lamarin da ke haifar da mummunar hasara ga tattalin arzikin kasar gami da hasarar rayuka da ake samu a duk shekara.(Ahmad)

Bello