logo

HAUSA

Sin ta gabatar da matakai 5 don inganta zirga-zirga masu dorewa a duniya

2021-10-15 20:44:49 cri

Sin ta gabatar da matakai 5 don inganta zirga-zirga masu dorewa a duniya_fororder_微信图片_20211015193814

“Dole ne mu bi yanayin ci gaba da duniya ke ciki, da inganta hadin gwiwar zirga-zirgar duniya, da rubuta sabon babi game da hadin kai a fannin manyan kayayyakin more rayuwa, da gudanar da cinikayya, da saka hannun jari mara shinge, da kuma yin mu’ammalar wayewar kai.” Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana hakan ne, a yayin jawabinsa a gun bikin bude babban taron zirga-zirga masu dorewa na kasa da kasa, na MDD karo na biyu ta kafar bidiyo, inda ya kuma gabatar da shawarwari guda biyar, da sanar da hakikanan matakan da za a dauka, wadanda suka nuna gudummawar da kasar Sin ke takawa, wajen inganta zirga-zirga masu dorewa na duniya, da nauyin da take dauka a matsayin wata babbar kasa.

A halin yanzu, kasar Sin tana samun ci gaba daga matsayinta na babbar kasa ta fuskar sufuri, zuwa kasa mai karfi a fannin, kuma tana inganta ci gaban zirga-zirga masu dorewa a duniya ta hanyar ci gaban da ta samu. Yanzu dai kasar Sin ta zama kasa mafi samun hada-hadar zirga-zirgar teku, da kuma yawan kayayyakin ciniki a duniya.

A cikin takardun hadin gwiwa sama da 200 da kasar Sin ta rattaba hannu kan su da kasashe 140, da kungiyoyin kasa da kasa 32, don raya shawarar "Ziri daya da hanya daya", yawancinsu sun shafi batun sufuri. Ciki kuwa ayyukan samar da ababen more rayuwa kamar layin dogo na China-Laos, da hanyar dogo mai saurin tafiya ta Jakarta-Bandung ta Indonesiya, da hanyar dogo ta Addis Ababa–Djibouti da dai sauransu, dukkansu sun kyautata yanayin sufuri na wurin, tare kuma da ciyar da zaman al’umma da tattalin arzikin wurin gaba.

A wannan taron kuma, shugaba Xi ya sanar da wani muhimmin mataki, inda ya ce kasar Sin za ta kafa cibiyar kirkire-kirkire, da ilmin zirga-zirga masu dorewa ta kasa da kasa. A ganin jakadan kasar Denmark a kasar Sin Thomas Østrup Møller, wannan yana nuna nauyi da alhakin da kasar Sin ta dauka, na hada kai da kasashen duniya, don inganta ci gaban sufuri na duniya, tare da taimakawa aiwatar da ajandar neman ci gaba mai dorewa ta MDD kafin shekarar 2030. (Mai fassara: Bilkisu)