logo

HAUSA

Sin ta tallafawa Burundi da alluran rigakafin cutar COVID-19

2021-10-15 20:46:56 CRI

Sin ta tallafawa Burundi da alluran rigakafin cutar COVID-19_fororder_96dda144ad345982c59996ac60d974a4cbef84b7

Kasar Sin ta baiwa Burundi tallafin rigakafin cutar numfashi ta COVID-19 har 500,000, samfurin kamfanin Sinopharm, domin tallafawa kasar a yakin da take yi da cutar.

An gudanar da bikin mika rigakafin a jiya Alhamis, a cibiyar shirin rigakafin kasar dake gundumar Mukaza, a birnin Bujumbura cibiyar hada hadar kasuwancin kasar, bikin da ya samu halartar jakadiyar Sin a Burundi Zhao Jiangping, da manyan jami’an hukumar lafiyar kasar, ciki har da ministan lafiya Thaddee Ndikumana.

Da yake tsokaci game da tallafin na Sin, minista Ndikumana, ya ce taimakon rigakafin ya kara jaddada dankon zumuntar gargajiya dake tsakanin Sin da Burundi. Ya kuma godewa Sin, bisa tallafin rigakafin da ta baiwa kasarsa.  (Saminu)