logo

HAUSA

Sin: Bai dace a raba kafa dangane da batun kare hakkin dan Adam ba

2021-10-14 10:58:32 CMG

Sin: Bai dace a raba kafa dangane da batun kare hakkin dan Adam ba_fororder_1014-bello-3

A jiya Laraba, mataimakin wakilin kasar Sin dake MDD, Dai Bing, a yayin wani taron da ya shafi aikin kare hakkin dan Adama na majalisar, ya ce, har yanzu annobar COVID-19 na ci gaba da bazuwa a duniya, kana matsaloli masu alaka da aikin lafiya, da bambancin yanayin ci gaba, da yadda ake nuna son kai a fannin neman samun alluran rigakafin COVID-19, suna haifar da kalubaloli ga aikin kare hakkin bil Adama. Saboda haka dole ne kasashe daban daban su kara hada kai, don tinkarar wadannan matsaloli.

A cewar jami’in na kasar Sin, kasarsa ba ta lamunci yadda ake neman siyasantar da batun hakkin dan Adam, tare da fakewa da batun don neman tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe, gami da yadda ake raba kafa dangane da batun kare hakkin bil Adama ba.

Mista Dai ya ce, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da sauran mambobin MDD da ofishin babban kwamishina mai kula da aikin kare hakkin dan Adam na majalisar, don neman ciyar da aikin kare hakkin dan Adam gaba. (Bello Wang)

Bello