logo

HAUSA

Babban sakataren MDD ya bukaci hadin kan duniya don rage afkuwar bala’u

2021-10-14 10:04:08 CRI

Babban sakataren MDD ya bukaci hadin kan duniya don rage afkuwar bala’u_fororder_1014-ahmad-1-UN

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bukaci hadin kan kasa da kasa da goyon bayan juna don rage afkuwar bala’u a duniya.

Cikin sakon da ya fitar ta kafar bidiyo don taya murnar ranar yaki da bala’u ta kasa da kasa wacce ta fado a ranar 13 ga watan Oktoba, mista Guterres ya ce, raunin shugabanci, karuwar talauci, lalata nau’ikan tsirrai, lalacewar muhallin halittu, da kuma yawan kaurar al’umma zuwa birane ba tare da an shirya hakan ba dukkan wadannan suna da alaka da juna wajen haddasa afkuwar bala’u.

Idan har aka ba da sanarwar gargadi game da yiwuwar fuskantar wata mummunar iska ko tsananin zafi cikin sa’o’i 24 gabanin faruwarsu hakan, to zai iya rage barnar da bala’un za su haifar da kusan kashi 30%. To sai dai kuma, mafi yawan kasashen duniya masu karami ko matsakaicin kudin shiga suna fama da matsalar karancin tsarin gargadi game da afkuwar bala’u. Don haka ingantaccen tsarin rage afkuwar bala’u ya dogara ne kan hadin gwiwa da goyon bayan kasa da kasa. Da gina wani tsari mafi dacewa da sauyin yanayi da rage afkuwar bala’u da rage hasarori, don haka abu mafi muhimmanci shi ne yadda za a dakile hasarar rayuka da hana lalacewar zaman rayuwa, da kawar da talauci da yunwa da kuma samar da dawwamaman ci gaba. (Ahmad)