logo

HAUSA

Sakataren MDD ya yi karin haske kan matakan gaggawa da ya dace a dauka a fannoni 3 don murmurewa daga COVID-19

2021-10-12 10:05:40 CRI

Sakataren MDD ya yi karin haske kan matakan gaggawa da ya dace a dauka a fannoni 3 don murmurewa daga COVID-19_fororder_1012-yaya-1.Korona

Babban sakataren MDD Antonio Guterres jiya Litinin ya yi karin haske kan matakan gaggawa da ya kamata a dauka a fannoni uku don fara murmurewa daga COVID-19 wanda zai amfani kowa, gami da kasashe mafiya rauni.

Na farko, ya yi kira da a dauki matakan rage matsalar bashi a kasashe da dama.

Na biyu, akwai bukatar tallafa wa gwamnatoci, musamman a kasashen da ke fama da rikice-rikice da masu rauni, don aiwatar da manufofin zamantakewa da tattalin arziki da ke gina aminci tare da ’yan kasarsu da kuma karfafa juriya kan bala'in da zai faru nan gaba, gami da matsalar sauyin yanayi.

Na uku, a cewar Guterres, idan har ana son cimma nasarar da duniya ke bukata cikin gaggawa, dole ne kasashen duniya su kasance masu ba da jagoranci. (Ibrahim Yaya)