logo

HAUSA

An bude taron COP15 a birnin Kunming

2021-10-11 20:18:33 CRI

An bude taron COP15 a birnin Kunming_fororder_1000

An bude taro na 15 na bangarorin da suka sa hannu kan yarjejeniyar kare nau’o’in halittu ta MDD wato COP15 da yammacin Litinin din nan, a birnin Kunming fadar mulkin lardin Yunnan, na kudu maso yammacin kasar Sin.

Taken taron na wannan karo shi ne "Wayewar kai game da muhallin halittu: Gina makomar bai daya ga daukacin halittun dake doron duniya". Taron COP15 dai shi ne irin sa na farko na kasa da kasa da MDD ke gudanarwa, wanda ke tabo batutuwa da suka jibanci wayewar kai game da muhallin halittu, wata mahanga da kasar Sin ta gabatar da ita.

Kasar Sin dai na cikin kasashen farko da suka sanya hannu kan yarjejeniyar kare nau’o’in halittu daban daban ta kasa da kasa, yarjejeniyar da kuma aka fara aiwatarwa a shekarar 1993. Yanzu haka yarjejeniyar na da mambobi 196, taron da ake gudunarwa kuma domin ta, shi ne dandali mafi tasiri na tattaunawa, da kuma yanke shawarwari game da ita.  (Saminu)