logo

HAUSA

Hua chunying: Sin mai karfin iko har kullum na da zarafi na ci gaba da kare al’ummunta

2021-09-27 19:42:21 CRI

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce kasar Sin mai karfi, karkashin jagorancin JKS, har kullum za ta ci gaba da kare al’ummun ta yadda ya kamata.

Hua ta yi wannan tsokaci ne a Litinin din nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, tana mai cewa, gwamnati da JKS na da karfin hali, da ikon kare hakkokin halal, da moriyar daukacin Sinawa da kamfanonin kasar.

Jami’ar ta kara da cewa, Amurka ta tsara abun da ta kira "taron dimokaradiyya ", musamman domin shata wata iyaka bisa akidun ta, tare da aiwatar da siyasar wariya, wadda za ta haifar illar rarrabuwar kawuna da fito na fito.  (Mai fassarawa: Saminu daga CRI Hausa)