logo

HAUSA

Darajar cinikayya tsakanin Sin da Afrika ta yi ta karuwa da kaso 14. 5 a kowacce shekara tun bayan kafa dandalin FOCAC

2021-09-27 10:39:44 CRI

Darajar cinikayya tsakanin Sin da Afrika ta yi ta karuwa da kaso 14. 5 a kowacce shekara tun bayan kafa dandalin FOCAC_fororder_0927China and Africa-Fa'iza

Hukumar kwastam ta kasar Sin, ta bayyana cewa, tun bayan kafuwar dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika na FOCAC, darajar cinikayya tsakanin bangarorin biyu ta karu daga yuan biliyan 87.37 a shekarar 2000, zuwa yuan triliyan 1.3 a shekarar 2020, inda a matsakaicin mataki aka samu karuwar kaso 14.5 a kowacce shekara.

Hukumar ta kara da cewa, yawan cinikayya tsakanin kamfanonin kasar Sin masu zaman kansu da nahiyar Afrika, ya karu daga yuan biliyan 4.76 a shekarar 2000, zuwa yuan biliyan 783 a 2020, inda ake samun karuwar kaso 29.1 a kowacce shekara. Haka kuma jarin kamfanonin a cinikayyar dake tsakanin Sin da Afrika, ya karu daga kaso 5.4 zuwa kaso 60.2. (Fa’iza Mustapha)