logo

HAUSA

An Bude Taron Dandalin Tattaunawa Kan Samun Ci Gaba Mai Dorewa Na Shekarar 2021

2021-09-27 12:29:55 CRI

An Bude Taron Dandalin Tattaunawa Kan Samun Ci Gaba Mai Dorewa Na Shekarar 2021_fororder_talauci

An bude taron dandalin tattaunawa na shekarar 2021 kan samun dawamammen ci gaba a birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin a jiya Lahadi, inda aka gabatar da “rahoton ci gaban kasar Sin dangane da aiwatar da ajandar MDD ta samun dawamammen ci gaba nan da shekarar 2030”.

Rahoton ya nuna cewa, a karshen shekarar 2020, kasar Sin ta cimma manufar fitar da mutane kusan miliyan 100 a yankunan karkara daga kangin talauci bisa shirin da ta tsara. Kasar Sin ta riga ajandar MDD shekaru 10 ta cimma burin kawar da talauci a shekarar 2030.

Daga shekarar 2016 zuwa 2019, matsakacin karuwar GDP na kasar Sin ta kai kaso 6.6 cikin dari a kowace shekara, gudummawar kasar Sin ga tattalin arzikin duniya ta kai kaso 30 cikin dari. Haka kuma a shekarar 2020, kasar Sin, ta kasance babbar kasa daya tilo a duniya, wadda ta samu ci gaban tattalin arziki.

Ya zuwa karshen shekarar 2020, kasar Sin ta kafa tsarin ba da tabbacin zamantakewar al’umma mafi girma a duniya. Yawan mutanen da suka samu inshorar lafiya a kasar ya wuce biliyan 1.36, yayin da yawan wadanda suka samu inshorar tsoffi ya kai kusan biliyan 1.

Haka zalika kasar Sin ta gaggauta sauya hanyar raya kanta ba tare da gurbata muhalli ba, ta aiwatar da kunshin yarjejeniyar tsarin MDD kan daidaita sauyin yanayi da yarjejeniyar Paris. Har ila yau, ta shiga ayyukan kasa da kasa kan daidaita sauyin yanayi cikin himma, tare da kara ba da nata gudummowa. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan