logo

HAUSA

Sin da Afirka sun kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa a fannonin abinci da amfanin gona na dallar Amurka miliyan 510

2021-09-27 15:17:20 CRI

Sin da Afirka sun kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa a fannonin abinci da amfanin gona na dallar Amurka miliyan 510_fororder_hoto

A yau Litinin, bayan aka kaddamar da bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka(CAETE) a karo na biyu a birnin Changsha, an kira taron dandalin tattauna hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ta fuskar abinci da amfanin gona a karo na farko.

A yayin taron, an yi bikin kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwar harkokin samar da abinci da amfanin gona a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, wadanda suka shafi dallar Amurka miliyan 510.

Wakilai na gwamnatocin kasashen Sin da Afirka da kamfanonin da abin ya shafa sama da 250 sun halarci wannan taro. (Maryam)