logo

HAUSA

An bude bikin hada hadar cinikayya ta yanar gizo na hajojin nahiyar Afirka karon farko a Changsha

2021-09-27 19:40:29 CRI

An bude bikin hada hadar cinikayya ta yanar gizo na hajojin nahiyar Afirka karon farko a Changsha_fororder_biki

A jiya Lahadi ne aka bude bikin hada hadar cinikayya ta yanar gizo, na hajojin nahiyar Afirka a karon farko, yayin taron baje koli karo na biyu na tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka, a birnin Changsha, fadar mulkin lardin Hunan.

Yayin taron na yini 3, wanda ake yadawa kai tsaye, an tsara amfani da dakunan yayata shirye shirye har guda 10, domin tallata hajojin nahiyar Afirka ga daukacin kasar Sin. Hajojin da za a tallata dai sun kunshi gahawa daga Habasha, da ridi daga Tanzania, da farin barkono daga Kamaru, da kuma giyar inabi daga Afirka ta kudu.  (Saminu)