logo

HAUSA

Sama da kasashe 60 sun nuna adawar su ga amfani da batun hakkin bil adama a matsayin hujjar tsoma baki cikin harkokin gidan Sin

2021-09-27 21:06:53 CRI

A ranar Juma’ar makon jiya, sama da kasashe 60 sun nuna adawar su ga amfani da batun hakkin bil adama, a matsayin hujjar tsoma baki cikin harkokin gidan Sin.

Kasashen sun gabatar da jawabin hadin gwiwa yayin zaman dandalin kare hakkin bil adama na MDD, a wani mataki na goyon bayan kasar Sin don gane da batutuwan da suka jibanci jihar Xinjiang, da yankin Hong Kong, da Tibet.

Game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, a yau Litinin ta ce matakin kasashen ya jaddada yadda gaskiya da adalci ke samun karbuwa a zukatan al’umma.

Hua Chunying ta ce dokar kasa da kasa da Amurka ke tallatawa, ba komai ta kunsa ba sai burin tsoma baki cikin harkokin sauran kasashen duniya, ta hanyar fakewa da batun ‘yanci da kuma dimokaradiyya. (Mai fassarawa: Saminu daga CRI Hausa)