logo

HAUSA

Tattalin arzikin intanet na kasar Sin ya kai yuan triliyan 39.2 a 2020

2021-09-27 10:51:31 CRI

Tattalin arzikin intanet na kasar Sin ya kai yuan triliyan 39.2 a 2020_fororder_0927digital economy-Fa'iza

Tattalin arzikin kasar Sin na kafofin intanet, ya karu zuwa RMB yuan triliyan 39.2, kimanin dala triliyan 6.07 a shekarar 2020, wanda ya dauki kaso 38.6 cikin dari na jimilar alkaluman tattalin arzikin kasar, inda kuma ya karu da kaso 9.7 a kan na shekarar 2019.

Wannan na kunshe ne cikin rahoton da cibiyar nazarin yanar gizo ta kasar Sin ta fitar yayin taron intanet na duniya da aka bude jiya a Wuzhen, dake lardin Zhejiang na gabashin kasar Sin.

A cewar rahoton, yawan hada-hadar kudi da aka yi ta intanet a kasar a shekarar 2020, ya kai RMB yuan triliyan 37.21, wanda ya karu da kaso 4.5 cikin dari a kan na 2019, yayin da kudin shigar bangaren cinikayya ta intanet ya kai RMB yuan triliyan 5.45, wanda ya karu da kaso 21.9 cikin dari a kan na shekarar 2019.

Rahoton ya kara da cewa, tattalin arzikin na intanet ya zama babban zabi ga kasashen duniya dake neman shawo kan tasirin annobar COVID-19 domin bunkasa sauye-sauyen tattalin arziki da zamantakewa, yana mai cewa, ya zama wani sabon kuzari ga ci gaban tattalin arzikin duniya. (Fa’iza Mustapha)