logo

HAUSA

Jaridar “The People’s Daily” ta wallafa wata makala mai taken dalilin da zai sa mu cimma nasara

2021-09-27 19:24:29 CRI

Jaridar “The People’s Daily”, mallakin kwamitin kolin JKS ta yau Litinin, ta wallafa wata makala a shafin ta na farko, mai taken "Dalilin da zai sa mu cimma nasara".

Makalar dai ta yi bita ne game da sauye sauyen da kasar Sin ta aiwatar a tarihin ta na tsawon karni, wadanda suka hada da farmakin mahara da aka taba kaddamawa kan kasar, har zuwa ci gaban da kasar ta samu a yau, da farfadowar ta, da ma irin karfi da ta samu.

Kaza lika, makalar ta amsa tambayoyi irin su "Mene ne dalilin da zai sa mu yi nasara" daga mahanga guda 3, wato tarihi, da ka’idojin ilimi, da ayyuka na zahiri.

Makalar ta hakaito kalamin shugaban kasar Xi Jinping, wanda ya taba bayyana cewa "Idan ba don JKS ba, da ba a kai ga cimma nasarar kafa sabuwar kasar Sin ba, kuma da ba a kai ga samun babban sauyi na farfadowar Sin ba, wanda a cewar makalar ita ce babbar amsa, bisa dalilai na hakika game da tambayar.

Har ila yau, makalar ta yi nuni da cewa, cikin muhimman tasirin ci gaban duniya da kasar Sin ta samar cikin lumana, a matsayin ta na mai kunshe da kaso 1 bisa 5 na daukacin al’ummar duniya, akwai shata sabuwar hanyar zamanantar da kasa, da kawowa bil adama sabon yanayi na wayewar kai, baya ga samar da dabarun da bil adama zai iya bi domin gina al’umma mai nagarta. (Saminu)