logo

HAUSA

Matasa mamallaka sana’o’i na Sin da Afirka sun tattauna game da hadin gwiwa da samar da ci gaba

2021-09-27 18:59:16 CRI

Matasa mamallaka sana’o’i na Sin da Afirka sun tattauna game da hadin gwiwa da samar da ci gaba_fororder_matasa

A jiya Lahadi ne matasa mamallaka sana’o’i daga tsagin Sin da nahiyar Afirka, suka tattauna game da hadin gwiwa da samar da ci gaba, karkashin dandalin kirkire kirkiren matasa da raya sana’o’i.

Matasan sassan biyu dai sun yi musayar ra’ayoyi ne a birnin Changsha, fadar mulkin lardin Hunan, a matsayin muhimmin aiki, cikin ayyukan dake karkashin yarjeniyoyin raya tattalin arziki da cinikayya da suka gudana, lokacin da ake tsaka da taron baje koli karo na 2, na raya tattalin arziki da cinikayyar Sin da Afirka.

An gudanar da dandalin matasan ne ta yanar gizo da kuma a zahiri, kuma ya samu halartar wakilan matasa mamallaka sana’o’i daga sama da kasashen Afirka 10, da suka hada da Kenya, da Benin, da Habasha, da Najeriya da Rwanda da sauran su, baya ga kasar Sin mai karbar bakuncin zaman. (Saminu)