logo

HAUSA

Jakadun Venezuela da Belarus na adawa da amfani da hakkin dan Adam don tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin

2021-09-25 17:03:40 CRI

Yayin taron majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD karo na 48 da aka gudanar a birnin Geneva, wakilin Pakistan ya yi jawabi a madadin wakilan kasashe 65, inda ya jaddada cewa, harkokin yankin Hong Kong, da jihar Xinjiang, da kuma yankin Tibet, harkokin cikin gida ne na kasar Sin, kuma bai kamata kasashen waje su tsoma baki cikinsu ba. Jakadun Venezuela da Belarus sun bayyanawa ‘yan jaridan babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG cewa, ya kamata a girmama ikon mulkin kasa da ‘yancin kai da kuma cikakkun yankunan kasa da kasa, a kaucewa tsoma baki kan harkokin cikin gida, inda suka ce wannan ita ce ka’idar kiyaye dangantaka tsakanin kasa da kasa.

Jakadun Venezuela da Belarus na adawa da amfani da hakkin dan Adam don tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin_fororder_0925-1

Zaunannen wakilin kasar Venezuela dake MDD a birnin Geneva ya bayyana cewa, kasarsa ta Venezuela ta na Allah wadai da Amurka da Canada da Birtaniya da kungiyar EU, saboda amfani da hakkin dan Adam da suka yi, don sakawa mutane da kungiyoyin jihar Xinjiang takunkumi ba bisa doka ba, kana sun yi amfani da siyasa don tsoma baki kan harkokin cikin gidan kasar Sin.

Jakadun Venezuela da Belarus na adawa da amfani da hakkin dan Adam don tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin_fororder_0925-2

A nasa bangare, zaunannen wakilin kasar Belarus dake MDD a birnin Geneva ya bayyana cewa, bayan Sin ta aiwatar da dokar kiyaye tsaron kasar a yankin Hong Kong a watan Yunin shekarar 2020, an samu babban sauyi a yankin Hong Kong, inda aka mayar da oda da doka da kuma kiyaye samun wadata a yankin. Don haka, an yi imanin cewa, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakan da suka dace, wadanda suka kawo zaman lafiya a yankin. (Zainab)