logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Nijar ya gana da babban wakilin shugaban kasar

2021-09-24 10:47:18 CRI

Jakadan Sin dake Nijar ya gana da babban wakilin shugaban kasar_fororder_1

Jiya Alhamis, jakadan kasar Sin dake janhuriyar Nijar Jiang Feng, ya gana da babban wakilin shugaban kasar, kuma mukadashin shugaban jam’iyyar PNDS mai mulki a kasar Foumakoye Gado.

Yayin tattaunawar su, jakada Jiang ya bayyana cewa, akwai aminci mai zurfi dake tsakanin Sin da Nijar, kuma sassan biyu sun samu babban sakamako, yayin da suke gudanar da hadin gwiwa a fannoni daban daban, lamarin da ya kawo babbar moriya ga al’ummun kasashen biyu baki daya, kuma jam’iyyu masu mulki na kasashen biyu, su ma suna gudanar da huldarsu yadda ya kamata. A nan gaba kuma, kasar Sin za ta ci gaba da kokari domin ciyar da hadin gwiwar sassan biyu gaba.

A nasa bangare, Foumakoye Gado ya taya jakadan Sin a kasarsa murnar kama aikin, inda ya bayyana cewa, huldar dake tsakanin kasashen biyu tana da inganci. Kaza lika a cewarsa gwamnatin Nijar na godewa tallafin da kasar Sin ta samar gare ta cikin dogon lokaci, kuma jam’iyyarsa tana mai da hankali matuka kan cudanyar dake tsakaninta da jam’iyyar JKS, tana kuma son kara zurfafa hadin gwiwa tsakanin jam’iyyun biyu.  (Jamila)