logo

HAUSA

Zhang Jun: Shawo kan kalubalen sauyin yanayi na bukatar aiki tare

2021-09-24 09:53:15 CRI

Zhang Jun: Shawo kan kalubalen sauyin yanayi na bukatar aiki tare_fororder_210924-Saminu1-zhangjun

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya ce tasirin sauyin yanayi kalubale ne na bai daya dake fuskantar daukacin bil adama, wanda kuma ke bukatar hadin gwiwar kasa da kasa wajen shawo kan sa.

Zhang Jun wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis, yayin da yake tsokaci game da batun sauyin yanayi da tsaro, ya ce yarjejeniyar MDD mai yaki da gurbata yanayi, da yarjejeniyar Paris mai nasaba da hakan, su ne jigon tunkarar wannan matsala.

Jami’in ya kara da cewa, kudurce aniya guda, tare da bin hanyoyi mabanbanta bisa ikon da kowa yake da shi, da yin aiki bisa daidaito, su ne muhimman ginshikai na shawo kan mummunan tasirin sauyin yanayi a matakin kasa da kasa.

Zhang ya ce, yana da muhimmanci ga kasashe masu tasowa, su cika alkawuran da suka dauka a matakin kasa da kasa yadda ya kamata. Duba da cewar kasashe masu tasowar bisa tarihi, na da nauyi a wuyansu na cika alkawuran.

Wakilin na Sin ya kara da cewa, ana da bukatar gaggauta aiwatar da kwararan matakai na ingiza manufar rage fitar da hayaki masu gurbata yanayi, da takaitawa, ko kawar da fitar da iskar carbon cikin sauri.

Kazalika ya zama wajibi a cewarsa, a samar da kudaden da ake bukata, don cimma nasarar ayyukan kyautata yanayi, da cike gibin da ake da shi na irin wadannan kudade da aka yi niyyar kashewa kafin shekarar 2020, kudaden da adadin su ya kai dalar Amurka biliyan 100.

Har ila yau, a samar da jadawali, da tabbataccen tsarin aiki na shekarar 2021 din nan zuwa ta 2025, a kuma samar da sabon shirin tattara kudade domin aikin, bayan shekarar 2025 dake tafe.  (Saminu)