logo

HAUSA

Xi Jinping Ya Gabatar Da Jawabin Taya Murnar Bude Dandalin Zhongguancun Na Shekarar 2021

2021-09-24 20:57:53 CRI

Xi Jinping Ya Gabatar Da Jawabin Taya Murnar Bude Dandalin Zhongguancun Na Shekarar 2021_fororder_1127898481_16324884589661n

A yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murnar bude dandalin Zhongguancun na shekarar 2021 ta kafar bidiyo

A jawabin nasa, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a duniyar da muke ciki a yau, tilas ne ci gaban kimiyya da fasaha ya kasance mai hangen nesa, ya fahimci yanayin da ake ciki, kuma ya bi sabbin bukatun samar da dan Adam da rayuwa. Xi ya ce, kasar Sin tana dora muhimmanci kan kirkire-kirkire na kimiyya da fasaha, tana kuma da kudurin inganta hadin gwiwar kirkire-kirkire na kimiyya da fasaha a duniya. Haka kuma kasar Sin za ta karfafa mu'amalar kasa da kasa a fannin kimiyya da fasaha tare da bude kofa, shiga cikin hanyoyin kirkire-kirkire na duniya, hadin gwiwa tare da inganta bincike na asali, inganta nasarorin kimiyya da fasaha, inganta sabbin fasahohi na ci gaban tattalin arziki, da karfafa ‘yancin mallakar fasaha, ilimin kimiyyar kira, tsara tunanin kimiyya da fasaha da nufin inganta tsarin gudanar da kimiyya da fasaha a duniya, da inganta habaka zamantakewar bil-Adama.

Xi Jinping ya jaddada cewa, Zhongguancun shi ne yankin farko na kasar Sin na nuna kirkire-kirkire kana dandalin Zhongguancun, shi ne dandalin kasa na musaya da hadin gwiwar fasahohin kimiyya da fasaha na duniya. Kasar Sin tana goyon bayan Zhongguancun wajen kaddamar da wani sabon zagaye na sauye-sauyen gwaji, da gaggauta gina rukunin kimiyya da fasaha da babu kamar sa a duniya, da bayar da sabbin gudummawa wajen inganta musaya da hadin gwiwa a fannin kimiyya da fasaha a duniya. (Ibrahim)

Ibrahim