logo

HAUSA

MDD ta fitar da kudin tallafin gaggawa domin taimakawa tsarin kiwon lafiya a kasar Afghanistan

2021-09-23 11:32:20 CRI

MDD ta fitar da kudin tallafin gaggawa domin taimakawa tsarin kiwon lafiya a kasar Afghanistan_fororder_0923F3-Afghanistan

MDD ta sanar da fitar da dala miliyan 45 na tallafin gaggawa domin kare tsarin kiwon lafiyar kasar Afghanistan daga rushewa.

Cikin sanarwar da aka fitar, an ce, mataimakin Sakatare Janar na majalisar mai kula da agajin jin kai, Martin Griffiths, ya ce kudin zai tafi ne ga ayyukan hukumar lafiya ta duniya da asusun kula da yara na majalisar, da tafiyar da harkokin cibiyoyin lafiya, ciki har da asibitocin dake kula da masu cutar COVID-19 a kasar, har zuwa karshen shekara.

Martin Griffiths ya kara da cewa, MDD ta kuduri niyyar taimakawa al’ummur Afghanistan a wannan lokaci da suke matukar bukata. (Fa’iza Mustapha)