logo

HAUSA

Sin ta bayyana manufar kare hakkin bil adama da sakamakon da ta samu a MDD

2021-09-23 13:50:15 CRI

Jiya Laraba ne, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Chen Xu ya yi cikakken bayani kan manufar kare hakkin bil adama ta kasarsa da sakamakon da ta samu a bangaren a gun taron tattaunawa karo na 48 na hukumar kare hakkin dan adama ta MDD, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi nasarar raya aikin kare hakkin bil adama mai salon musamman, yanzu haka ta riga ta cimma burin gina al’umma mai matsakaicin wadata daga duk fannoni a fadin kasar, kana ta yi nasarar daidaita matsalar talauci, ana iya cewa, ta samu babban sakamako wajen kare hakkin bil adama.

Jami’in ya kara da cewa, kwanan baya gwamnatin kasar Sin ta fitar da “shirin kare hakkin bil adama na kasar” domin tabbatar da hakkin bil adama na al’ummun kasar, tana kuma son hada kai da sauran kasashen duniya domin ingiza gina al’umma mai kyakkyawar makoma a fadin duniya baki daya.(Jamila)