logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Sin ya halarci bikin cika shekaru 20 da yarjejeniyar Durban

2021-09-23 11:12:42 CRI

Ministan harkokin wajen Sin ya halarci bikin cika shekaru 20 da yarjejeniyar Durban_fororder_0923A2-Wangyi

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, a ranar Laraba ya halarci babban taron tunawa da cika shekaru 20 da kulla yarjejeniyar Durban ta kafar bidiyo inda ya gabatar da jawabi.

Wang ya ce, yarjejeniyar Durban wata muhimmiyar matsaya ce dake shafar dukkan kasashen duniya. Kasar Sin ta bukaci a karfafa tattaunawa da yin cudanya a tsakanin kabilu daban daban da mabambantan al’adu, kana ta bukaci a tabbatar kowane mutum ya ci moriyar hakkin cigaba, da kawar da nuna bambancin yankuna do yakar manyan kalubaloli kamar talauci, da danniya, da shiga a dama da kowa harkokin zamantakewa da kawar da gibin tattalin arziki.

Kasar Sin za ta ci gaba da yin aiki tare da sauran kasashe domin sa kaimi a kokarin kawar da dukkan batutuwan nuna wariya da kuma kokarin gina tsarin duniya mai samar da daidaito ga kowane bil Adama. (Ahmad)