logo

HAUSA

An kaddamar da bude gasar wasannin kasa karo na 14

2021-09-16 16:31:37 CRI

An kaddamar da bude gasar wasannin kasa karo na 14_fororder_src=http___upload.mnw.cn_2021_0916_1631756969271.png&refer=http___upload.mnw

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kaddamar da bude gasar wasannin kasa karo na 14

Da yammacin Larabar nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya kaddamar da gasar wasannin kasa karo na 14, a filin wasa na Xi'an Olympic Center.

Gasar wadda ake yiwa lakabi da "Karamar Olympics", ana gudanar da ita ne duk bayan shekaru 4, an kuma fara gudanar da ita ne tun daga shekarar 1959, ta kuma kunshi wasanni da dama masu salon gasar Olympics, baya ga gasar fasahar fada ta Wushu irin ta Sin.

A bana ana sa ran halartar sama da ‘yan wasan motsa jiki sama da 12,000 daga sassa daban daban na kasar, za ta kuma gudana har zuwa ranar 27 ga watan nan na Satumba.  (

Cinikin ‘Yan Wasa: Za A Kafa Dokar Kashe Kudi A Nahiyar Turai – FIFA

Bayan da aka kammala cin kasuwar saye da sayar na ‘yan wasa ta bana, ana ci gaba da nuna damuwa wajen yadda manyan kungiyoyi musamman a kasashen Ingila da Sipaniya da Faransa da Jamus da kuma kasar Italiya suke kashe makudan kudade wajen sayan manyan ‘yan wasa wanda hakan yana hana kananan kungiyoyi fafatawa a kasuwar saboda yadda aka sangarta kungiyoyi da sayan ‘yan wasansu masu tsada.

A wani taron manema labarai da ya yi, shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Gianni Infantino ya bayyana cewa hukumar za ta saka kafar wando daya da kungiyoyin da suke wuce gona da iri wajen kashe kudi a kasuwar saye da sayar na ‘yan wasa.

Kungiyiyon gasar Premier League na kasar Ingila sun kashe makudan kudade wajen ganin sun kara karfi domin tunkarar kakar wasa wadda tuni aka riga aka fara kuma har an buga wasanni biyu-biyu wasu kuma uku-uku.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta sayo ‘yan wasa irinsu Jadon Sancho a kan kudi fam miliyan 73 daga Borussia Dortmund da dan kwallon tawagar Faransa, Raphael Barane daga Real Madrid kan fam miliyan 34 sai kuma dan wasa Cristiano Ronaldo da ya koma kungiyar a kan kudi fam miliyan 25.

 Mai rike da kofin Premier League, Manchester City ta kafa tarihin daukar dan wasa mafi tsada a Birtaniya, inda ta sayo Jack Grealish daga kungiyar kwallon kafa ta Aston Billa kan kudi fam miliyan 100.

Kawo yanzu da aka kammala cinikayyar ‘yan wasan tun a ranar 31 ga watan Agustan da ya gabata, kungiyoyin Premier League sun kashe kudi fam biliyan 962 wajen sayo ‘yan wasa a bana bayan da a bara aka kashe fam biliyan 1.3 wajen sayan ‘yan wasan.

Mai rike da kofin zakarun Turai na Champions League, Chelsea ita ce ta biyu wajen sayen dan kwallo da tsada, bayan da ta sake daukar dan wasa Romelu Lukaku daga kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan kan fam miliyan 97.5 kuma cinikin ‘yan wasa shida da aka yi mafi tsada a Birtaniya.

A dukkan hada-hadar da aka yi a kasuwannin Ingila ce kan gaba da ta dauki Jack Grealish daga Aston Billa kan fam miliyan 100, sannan a gasar La Liga Atletico Madrid ce ta sayi Rodrigo de Paul daga Udinese kan fam miliyan 30 a matakin mafi tsada a Sifaniya.

Tammy Abraham wanda ya koma kungiyar kwallon kafa ta Roma daga Chelsea kuma an saye shi ne a kan kudi fam miliyan 34, sannan shi ne wanda aka dauka a kasar Italiya mafi tsada a bana.

A Bundesliga kuwa ta kasar Jamus, Bayern Munich ce ta dauki dan kwallo mafi tsada wato Dayot Upamecano daga kungiyar kwallon kafa ta RB Leipzig wadda ita ma take buga wasa a Jamus a kan kudi fam miliyan 36.

Achraf Hakimi wanda ya koma Paris St Germain daga Inter Milan kan fam miliyan 51, shi ne wanda aka saya mafi tsada a Faransa a bana, sai kuma Lionel Messi wanda ya koma PSG daga Barcelona a matakin wanda bai da yarjejeniya bayan da kwantiraginsa ya kare a Barcelona.

Ga jerin cefane biyar-biyar mafiya tsada da aka yi a Premier da La Liga da Serie A da Bundesliga da kuma Ligue 1 a bana.

Manyan Cefane Biyar A Premier League:

Jack Grealish shi ne aka dauka mafi tsada a Birtaniya kan fam miliyan 100 daga Aston Billa, sai Romelu Lukaku daga kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan zuwa Chelsea Chelsea kan fam miliyan 97.5

Akwai kuma Jadon Sancho daga kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund zuwa Manchester United kan fam miliyan kan fam miliyan 73 sai Ben White daga Brighton zuwa Arsenal kan fam miliyan 50, sannan akwai cinikin Raphael Barane daga Real Madrid zuwa Manchester United fam miliyan 34.

Manyan Cefane Biyar A La Liga:

Rodrigo de Paul daga Udinese zuwa Atletico Madrid kan fam miliyan 30, sai Eduardo Camabinga daga Rennes zuwa Real Madrid kan fam miliyan 26, sanna sai Matheus Cunha daga Hertha Berlin zuwa Atletico Madrid kan fam miliyan 25, sai Arnaut Danjuma daga Bournemouth zuwa Billarreal kan fam miliyan 20, a karshe kuma akwai cinikin Rafa Mir daga Huesca zuwa Sebilla kan fam miliyan 13.

Manyan Cefane Biyar A Serie A:

Tammy Abraham daga Chelsea zuwa Roma kan fam miliyan 34, sai Fikayo Tomori ya koma AC Milan daga Chelsea a kan kudi fam miliyan 24, sannan sai Nicolas Gonzalez daga Stuttgard zuwa Fiorentina kan fam miliyan 20, sai Weston McKennie daga Schalke 04 zuwa Juventus kan fam miliyan 18 sai kuma Juan Musso daga Udinese zuwa Atalanta kan fam miliyan 17.

Manyan Cefane Biyar A Bundesliga:

Dayot Upamecano daga RB Leipzig zuwa Bayern kan fam miliyan 36, sai cinikin Donyell Malen daga PSB Eindhoben zuwa Dortmund kan fam miliyan 25, sannan sai Odilon Kossounou daga Club Brugge zuwa Bayer Leberkusen kan fam miliyan 19, har ila yau, akwai cinikin Andre Silba daga Eintracht Frankfurt zuwa RB Leipzig kan fam miliyan 19, sai kuma Josko Gbardiol daga Dinamo Zagareb zuwa RB Leipzig kan fam miliyan 16.

Manyan Cefane Biyar a Ligue 1:

Achraf Hakimi daga Inter Milan zuwa Paris St Germain kan fam miliyan 51, sai kuma Gerson daga Flamengo zuwa Marseille kan fam miliyan 21, sannan sai cinikin Myron Boadu daga AZ Alkama zuwa Monaco kan fam miliyan 14, sai cinikin Loic Bade daga Paris FC zuwa Rennes kan fam miliyan 14, sai kuma cinikin da akayi na Danilo Pereira daga FC Porto zuwa Paris St Germain kan fam miliyan 13.

Sai dai bayan korafe-korafen da hukumar kwallon kafa ta duniya ta samu a kan yanayin yadda manyan kungiyoyi suka lalata kasuwar da bayar da makudan kudade wajen sayan ‘yan wasa, ya sa Hukumar FIFA ta bayyana cewa za ta fara kayyade kudaden da kungiya za su dunga kashe a kasuwar saye da sayar na ‘yan wasa wanda hakan zai sa kananan kungiyoyi suma su samu damar sayan ‘yan wasa.

A kwanakin baya dai, Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Turai ta yi barazanar fara hukunta kungiyoyin da suke kashe makudan kudade wanda hakan ya sa ake ganin manyan kungiyoyi irinsu PSG da Manchester City da Real Madrid da Manchester United da Chelsea za su fuskanci matsinlamba.

Sai dai abu ne mai wahala wannan doka ta yi aiki, saboda yadda kungiyoyin suke da karfin fada a ji a harkar kwallon kafa da kuma karfin tattalin arzikin da kungiyoyin suke da shi a duniya.