logo

HAUSA

Kwararriyar Masar: Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ta Rika Kafa Sabbin Hanyoyin Dinke Duniya Baki Daya

2021-09-10 11:02:54 CRI

Kwararriyar Masar: Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ta Rika Kafa Sabbin Hanyoyin Dinke Duniya Baki Daya_fororder_masar

A bana ne aka cika shekaru 8 da kasar Sin ta gabatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”. Ya zuwa watan Agustan bana, kasar Sin ta daddale takardun hadin gwiwar aiwatar da shawarar fiye da 200 tare da kasashe ko kungiyoyin kasa da kasa 172. Shawarar ta kasance hajar da kowa zai yi amfani da ita a duniya, wadda ta samu karbuwa tsakanin kasa da kasa, kana kuma ta zama dandalin hadin gwiwa mafi girma a duniya.

Nadia Helmy, shehun malamar ilmin siyasa a jami’ar Beni Suef ta kasar Masar kuma wata kwararriya kan batutuwan da suka shafi kasar Sin ta yi bayani da cewa, sakamakon aiwatar da shawarar, ya sa kasar Sin ta rika kafa sabbin hanyoyin samun wadatuwar tattalin arziki da ciniki tsakanin kasa da kasa da zurfafa hadin gwiwa a shiyya-shiyya da kara azama kan dinkewar duniya baki daya mai kunshe da kowa. Yayin da annobar COVID-19 ke yaduwa a sassan duniya, hanyar siliki ta kiwon lafiya tana taka muhimmiyar rawa wajen rage radadin annobar da fita daga annobar da farfado da tattalin arziki. Inda ta ce, “Bisa shawarar, kuma karkashin tsarin hanyar siliki ta kiwon lafiya, kasar Sin tana taimakawa kasa da kasa, ta hada kai da kasashen duniya wajen nazarin rigakafi, samar da marufin hanci da baki, ba da agajin lafiya da dai sauransu, a kokarin rage radadin annobar ta fuskar kiwon lafiya da tattalin arziki, lamarin da ya nuna tunanin raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan dan Adam. Don haka shawarar na da muhimmanci matuka, wadda ake aiwatar da ita bisa ka’idar taimakawa juna, wadda ta kasance hanya mafii dacewa a duniya bayan barkewar annobar.”  (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan