logo

HAUSA

Wang Yi ya halarci taron kara wa juna sani kan tunawa da cika shekaru 50 da dawowa da kasar Sin kujerarta a MDD

2021-09-08 14:12:31 CRI

Wang Yi ya halarci taron kara wa juna sani kan tunawa da cika shekaru 50 da dawowa da kasar Sin kujerarta a MDD_fororder_src=http---n.sinaimg.cn-spider20210908-279-w689h390-20210908-efd6-ff66239fa2f92e60d311a65387be32d1&refer=http---n.sinaimg

A yau Laraba, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya halarci taron kara wa juna sani kan tunawa da cika shekaru 50 da dawowa da  Jamhuriyar Jama’ar Sin kujerarta a MDD ta bidiyo.

A cikin jawabin da ya bayar a gun taron, Wang ya bayyana cewa, ya kamata bangarori daban daban su cimma matsaya daya kan wasu batutuwa. Da farko dai, ya kamata a nace ga bin tsarin kasancewar bangarori da dama don kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. Na biyu shi ne, a inganta hadin kai don yaki da cutar COVID-19, a kokarin ba da kariya ga lafiyar bil Adam. Na uku shi ne a mayar da batun samun ci gaba a gaban komai, a yi kokarin sa kaimi ga samun wadatar kasa da kasa gaba daya. Na hudu, a dauki ra’ayin bude kofa da ma hakuri da juna. Na biyar, a kyautata aikin daidaita muhalli, a yi kokarin samun kyakkyawar duniya mai tsabta. Na karshe kuma shi ne a kara cudanyar juna domin kara azama ga ci gaban wayewar kan bil Adama.(Kande Gao)