logo

HAUSA

Darussan da aka koya a gasar Olympics ta birnin Tokyo

2021-08-11 09:57:24 CRI

Ranar Lahadi 8 ga watan Agustan shekarar 2021 ne, aka kammala gasar wasannin motsa jiki ta Olympics karo na 32 a birnin Tokyon kasar Japan. A baya dai an shirya gudanar da gasar ce a shekarar 2020, amma aka dage ta sakamakon barkewar annobar COVID-19 dake ci gaba da addabar sassan duniya.

Darussan da aka koya a gasar Olympics ta birnin Tokyo_fororder_210811世界21030-hoto1

Kimanin matune 950 ne, ciki har da jami’ai da ’yan jarida aka bari suka shiga wajen bude wasannin mai daukar mutane kusan dubu 10. Gasar wasanni ta Tokyo, ta janyo hankalin ’yan wasa 11,000 daga tawagogi 205 da kungiyar wasannin Olympics ta ’yan gudun hijira.

Kasar Sin ta tura tawaga mai kunshe da mambobi 777 zuwa Tokyo, kuma wannan ita ce tawaga mai kunshe da mutane mafi yawa da ta taba turawa zuwa ketare. ’Yan wasan kasar Sin 431 ciki har da zakarun wasannin Olympics 24 ne, suka fafata a wasanni 30 daga cikin 33 da ka fafata a gasar birnin Tokyo.

Darussan da aka koya a gasar Olympics ta birnin Tokyo_fororder_210811世界21030-hoto2

Shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olmypics na kasa da kasa Thomas Bach ya ce, nasarorin da ’yan wasan kasar Sin suka cimma a wasanni daban-daban ta yi matukar birge shi, kuma hakan zai kara nunawa duniya yadda kasar Sin ke bunkasa cikin sauri. Ya kuma yi imanin cewa, gasar Olympics ta birnin Beijing da za a gudanar a lokacin hunturun shekarar 2022 za ta kayatar da duniya.

Kasar Amurka ce ta jagoranci teburin lambobin da aka lashe, inda ta samu lambar zinare 39, azurfa 41, tagulla 33. Sai kasar Sin dake biya mata baya da zinare 38, azurfa 32, da tagulla 18, Japan ce ta uku. Kasar Kenya ta zo ta 19, Uganda ta 36, Afirka ta kudu ta zo ta 52, yayin da Najeriya ta yi ta 74, inda ta lashe Azurfa 1 da Tagulla 1. A ranar 5 ga watan Satumban shekarar 2021 ne, za a gudanar da gasar Olympics ajin nakasassu a birnin na Tokyo. Wannan ita ce gasar Olympics ta 2 da aka gudanar a kasar Japan. (Saminu,Ibrahim/Sanusi Chen)