logo

HAUSA

Sin na fatan Amurka za ta sauya mummunan tunanin ta

2021-07-26 12:18:49 CRI

Sin na fatan Amurka za ta sauya mummunan tunanin ta_fororder_0726China-Saminu

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Xie Feng, ya ce alakar Sin da Amurka ta hadu da cikas, sakamakon yadda wasu Amurkawa ke yayata Sin a matsayin abokiyar gaba. Xie Feng na ganin lokaci ya yi da Amurka, za ta yi watsi da wannan mummunan tunani, da manufofi masu hadarin gaske.

Xie ya yi wannan tsokaci ne a yau, yayin zantawarsa da mataimakiyar ministan harkokin wajen Amurka Wendy Sherman, wadda ke ziyarar aiki a ranekun Lahadi da Litinin din nan a birnin Tianjin.

Xie ya ce Amurka na aiwatar da manufofi uku masu hadari, wato takara, da hadin gwiwa da fito na fito, wadanda babban makasudinsu shi ne dakile kasar Sin. Amurka na fatan fito na fito da kasar Sin zai ba ta damar cimma babban burinta, yayin da hadin gwiwa zai saukaka mata cimma nasara, kana takara ta zame mata tarko da take amfani da shi wajen haifar da hargitsi.

To sai dai kuma a cewar jami’in na Sin, idan Amurka na fatan yin hadin gwiwa da Sin yadda ya kamata, ya dace ta yi hakan bisa gaskiya. Ta yi amfani da sassa da take da fifiko cikin su, wajen inganta shigar da hajoji, da kawar da takunkumin cinikayya. Kuma bai kamata ta yi amfani da rikici ko fito na fito wajen dakile ci gaban kasar Sin ba.

Xie Feng ya kara da cewa, ta hanyar mayar da kan ta ’yar sandar duniya, Amurka na yunkurin mayar da dokoki da ka’idojinta na gida, da na wasu tsirarun kasashen yamma a matsayin dokokin kasa da kasa, tare da kullewa da dakushe sauran kasashe. Kaza lika suna dagewa wajen tankwara ka’idojin sauran sassa, da yunkurin cimma gajiyar kashin kai. A hannu guda kuma, suna son rungumar salon danniya, ta yadda masu karfi za su farauci marasa karfi, kuma manya za su ci zalin kanana.   (Saminu)