logo

HAUSA

Zimbabwe ta karbi karin alluran rigakafin COVID-19 daga kasar Sin

2021-07-26 09:38:31 CRI

Zimbabwe ta karbi karin alluran rigakafin COVID-19 daga kasar Sin_fororder_210726-Zimbabwe-Fa'iza

Zimbabwe ta karbi kashi na 6 na alluran rigakafin COVID-19 daga kasar Sin, yayin da kasar dake kudancin Afrika ke kara matsa kaimi wajen yi wa al’ummarta rigakafi da zummar dakile ci gaba da yaduwar cutar.

Alluran na baya-bayan nan sun isa ne a lokacin da kasar ke kara inganta shirinta na yi wa mutane rigakafi, bisa la’akari da barkewar cutar a zagaye na 3, inda adadin wadanda ta yi ajalinsu a kasar ya karu zuwa sama da 3,000.

Zuwa yanzu, mutanen da ya yawansu ya kai 97,277 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar, ciki har da 64,628 da suka warke.

A cewar ministan kudin kasar Mthuli Ncube, ana sa ran samun karin riga kafin daga kasar Sin a ranar Alhamis, haka kuma a cikin watan Augusta.

Zuwa karshen bana, kasar na da burin yi wa a kalla mutane miliyan 10 daga cikin al’ummarta miliyan 14 allurar rigakafin, domin samun mutane masu dimbin yawa dake da karfin garkuwar jiki. (Fa’iza Mustapha)