logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Najeriya ya gana da karamin ministan raya ma’addinai da karafa na Najeriya

2021-07-26 11:10:05 CRI

Jakadan Sin dake Najeriya ya gana da karamin ministan raya ma’addinai da karafa na Najeriya_fororder_微信图片_20210726110941

Jakadan Sin dake Najeriya Cui Jianchun ya gana da karamin minista mai kula da harkokin raya ma’addinai da karafa na Najeriya Dr. Uchechukwu Ogah.

Jakadan ya nuna cewa, Sin da Najeriya suna da daddaden zumunci a tsakaninsu, kuma suna samun ci gaba mai armashi a hadin gwiwarsu a bangarori daban-daban. Ya ce yayin da aka cika shekaru 50 da kafuwar dangantakar diplomasiyyarsu a tsakaninsu a bana, Sin na fatan inganta hadin gwiwar kasashen biyu a fannin zuba jari ta fuskar ma’addinai da sauransu, ta yadda za a amfanawa jama’ar kasashen biyu yadda ya kamata.

A nasa bangare, Dr. Uchechukwu Ogah ya bayyana cewa, Sin sahihiyar abokiyar Najeriya ce da za a iya dogaro da ita. Kuma Nijeriya na da albalkatun ma’addinai masu yawa, don haka kasar na fatan kara yin gadin gwiwa da kasar Sin ta fuskar hakar ma’addinai don samun ci gaba tare. Ya kara da cewa, yana maraba da kamfanonin hakar ma’adinai na Sin da su zuba jarinsu a kasar nan gaba. (Amina Xu)