logo

HAUSA

Sarah Marjorey Kisakye: Da fatan zan iya samar da gudummawata ga karfafa dankon zumunci a tsakanin Sin da Afirka

2021-07-26 14:25:52 CRI

Sarah Marjorey Kisakye: Da fatan zai iya samar da gudummawata ga karfafa dankon zumunci a tsakanin Sin da Afirka_fororder_莎拉参观长城(受访者供图)

A farkon wannan wata, Sarah Marjorey Kisakye, ’yar kasar Uganda ta kammala karatun digiri na biyu a jami’ar koyon ilmin watsa labarai ta kasar Sin. Kafin zuwanta kasar Sin, kasancewarta ’yar jarida, malama Sarah ta taba samar da rahotanni dangane da kasar. To bayan shafe tsawon shekaru biyu tana karatu da ma rayuwa a kasar, ko akwai karuwar da ta samu? Abokiyar aikinmu Lubabatu na tare da karin haske.

A shekarar 2019, Sarah Marjorey Kisakye ta zo kasar Sin daga kasar Uganda da ke gabashin Afirka, don ta kara ilmi dangane da ilmin watsa labarai na kasa da kasa a jami’ar koyon ilmin watsa labarai ta kasar Sin da ke birnin Beijing.

Kafin zuwanta kasar Sin, Sarah ta shafe tsawon shekaru biyar tana aikin jarida a kasar Uganda. Kamar dai dimbin bakin da ba su taba zuwa kasar Sin ba, Sarah ta fara sanin kasar Sin ne da dabbar Panda mai ban sha’awa. Don haka, zuwanta kasar ke da wuya, sai ta kai ziyara gidan dabbobi. Ta ce,“Dabbobi masu yawa na gani a gidan dabbobi na birnin Beijing, sai dai daga cikinsu Panda sun fi burge ni. Na taba ba da rahoton Panda a kasarmu Uganda, amma ban taba gani da idona ba. Don haka, na yi matukar farin cikin ganinsu da idona.”

Bayan ta dade tana rayuwa da dalibta a kasar Sin, Sarah ta kuma kara fahimtar kasar, kuma nau’o’in abincin kasar iri-iri sun burge ta matuka, musamman ma gasasshiyar agwagwa. Tana mai cewa,“Kasar Sin na da nau’o’in abinci iri iri, ciki har da wasu da mu ma mu kan ci a kasarmu. Abokaina sun kai ni wurin cin gasashiyyar agwagwa, gaskiya a da ban yi zaton agwagwa na da dadi sosai ba, amma da na dandana, na ji dadinta.”

Bayan zuwanta kasar Sin, Sarah ba ta yi watsi da aikinta ba, inda ta ci gaba da bayyana wa al’ummar kasar Uganda abubuwan da ta gani a kasar Sin. Ta ce,“A takaice dai, al’ummar Uganda suna sha’awar labaran da suka shafi tattalin arziki, sabo da akwai ’yan kasar Uganda da yawa da suke yin ciniki a kasar Sin. Baya ga haka, aikin gona ma abu ne da ke jan hankalinsu, kasancewar aikin gona daya daga cikin ginshikan tattalin arzikinmu. Ban da haka, aikin samar da ilmi da huldar da ke tsakanin Uganda da kasar Sin da ma huldar dake tsakanin Afirka da kasar Sin duk suna daukar hankalinsu.”

A sakamakon annobar Covid-19, Sarah ba ta samu damar zagaya sauran sassan kasar Sin ba ban da birnin Beijing. Amma abin farin ciki shi ne, kwanan nan ta samu damar zuwa gundumar Xing da ke birnin Lvliang na kasar, ziyarar da kungiyar sada zumunta tsakanin al’ummar kasar Sin da na kasashen waje ta shirya, inda Sarah tare da wakilan matasan Afirka da suka zo daga kasashen Afirka 13 suka ziyarci masana’antun saukaka fatara, tare kuma da koyon fasahar gargajiya ta yanka takarda ta wurin da sauransu. Sarah ta ce, ziyarar ta ba ta damar kara fahimtar fasahohin kasar Sin a fannin saukaka fatara. Yadda sana’o’in saukaka fatara ke bunkasa a wurin ya burge ta sosai, baya ga kuma yanayi mai ni’ima na wurin da ya tunatar da ita garin da ta fito. Tana mai cewa,“Tsaunuka da kauyuka da kuma masara da aka shuka a cikin gonaki, duk sun sa na tuna da garinmu.”

Shekaru biyu ke nan da Sarah ta baro gida, amma ba ta manta da abin da ya kawo ta kasar Sin ba, wato kara ilmi tare kuma da karfafa fahimtar juna a tsakanin Afirka da kasar Sin. Tana kuma fatan bayyana fasahohin kasar Sin ta fannin samun ci gaba ga karin al’ummar Uganda, haka kuma tana fatan taimaka wa karin al’ummar Sinawa fahimtar Afirka. Ta ce,“A kan yi zaton Afirka a matsayin wurin da ke da namun daji a ko ina. Haka ne, akwai namun daji da yawa a Afirka, sai dai ba su cikin birane. Amma akwai wuya a fahimtar da wadanda ba su taba zuwa Afirka ba. Don haka na kan nuna musu hotunan bidiyo, kuma bayan sun kalla, su kan ce, ashe, akwai manyan gine-gine ma a Afirka. Ni kuma sai in ce, Afirka ma na tafiya tare da zamani.”

Don haka, Sarah ta yanke shawarar ci gaba da karatun digiri na uku a kasar Sin, kuma a watan Satumban bana, za ta fara karatun na shekaru hudu a jami’ar koyon ilmin watsa labarai ta kasar Sin. Ta ce,“Huldar da ke tsakanin Sin da Uganda, da huldar da ke tsakanin Sin da Afirka, da saukaka fatara da aikin ilmantarwa da walwalar yara, dukkansu na cikin abubuwan da nake fatan yin nazari da ma yin rubuce-rubuce kan su.”

Sarah ta kara da cewa, bayan da ta kammala karatu, tana fatan za ta iya samar da gudummawarta wajen inganta huldar da ke tsakanin Sin da Uganda da ma huldar da ke tsakanin Sin da Afirka. (Lubabatu)