logo

HAUSA

An ceto dalibai 28 da aka sace a Nijeriya

2021-07-26 09:39:18 CRI

Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta bada tabbacin ’yan bindiga sun saki dalibai sama da 28 da suka sace daga makarantar sakandare ta jihar Kaduna dake arewa maso yammacin kasar.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an saki daliban ne da daren ranar Asabar, kuma yanzu haka ana shirye-shiryen mika su ga iyalansu.

Ya kara da cewa, suna daga cikin daliban da ba a san adadinsu ba, da aka yi awon gaba da su daga makarantar Bethel Baptist dake Kaduna a ranar 5 ga wata, bayan harin da wasu gungun ’yan bindiga suka kai makarantarsu.

Sai dai Mohammed Jalige, ya ki yin karin bayani game da yadda aka saki daliban, ko an biya kudin fansa, ko a’a. (Fa’iza Mustapha)