logo

HAUSA

Shugaban Tunisia ya sallami firaministan kasar tare da dakatar da majalissar wakilai

2021-07-26 09:50:21 CRI

Shugaban Tunisia ya sallami firaministan kasar tare da dakatar da majalissar wakilai_fororder_0726-Tunisian president-Saminu

Shugaban Tunisia Kais Saied, ya sallami firaministan kasar Hichem Mechichi, tare da dakatar da daukacin ayyukan majalissar wakilai. A hannu guda kuma ya dage dukkanin kariyar doka da ’yan majalissar wakilan ke da ita.

Shugaba Saied ya bayyana hakan ne yayin wata sanarwa ta kafar bidiyo, wadda aka fitar kan shafin facebook na fadar shugaban kasar, bayan kammala wani zaman musamman da manyan shugabannin hukumomin tsaron kasar. Mr. Saied ya ce zai kasance shugaban gwamnatin kasar na rikon kwarya, har zuwa lokacin da za a nada sabon firaminista.

Rahotanni na cewa, a jiya Lahadin zanga zanga ta barke a larduna da dama na Tunisia, bayan korafin tabarbarewar harkokin kiwon lafiya, da tattalin arziki, da na zamantakewar al’ummar kasar, inda masu boren ke kira da a rushe gwamnatin kasar mai ci, da majalissar wakilai karkashin jagorancin Rached Ghannouchi, wanda ke shugabantar jam’iyyar Ennahdha. (Saminu)