logo

HAUSA

Sin: Amurka ce kwararriya a fannonin diflomasiyyar matsin lamba

2021-07-26 16:45:52 CRI

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Xie Feng, ya ce ko shakka babu Amurka ce kwararriya a fannin kirkira, da mallakar fasahar diflomasiyyar matsin lamba.

Xie ya bayyana hakan ne, yayin zantawarsa da takwararsa ta Amurka Wendy Sherman, a yau Litinin a birnin Tianjin, a ci gaba da ziyarar aikin yini biyu da Sherman din ke yi.

Jami’in kasar Sin ya kara da cewa, "Sin ba ta taba matsawa wata kasa lamba ba, kuma tana yin martani ga duk wani mataki na shisshigin kasashen waje, ta hanyar amfani da dokoki da ka’idoji mafiya dacewa, domin kare hakkokin ta da moriyarta, da kuma wanzar da daidaito da adalci a mataki na kasa da kasa.

Xie ya kara da cewa, Sin ba ta taba zuwa kofar wata kasa da nufin ta da husuma ba. Kana ba ta taba shigar da makaminta wata kasa ta waje ba, ba ta taba kuma mamaye yankin wata kasa ba.

Jami’in ya kara da cewa, har kullum Amurka ce ke kakabawa sauran sassa takunkumi, da shigar da makamai sauran kasashe, tare da tsoma hannu cikin harkokin wajen wasu kasashen na daban.

Bugu da kari, manufar Amurka na kutse da karfi cikin sauran kasashen waje, wani nau’i ne na nuna fin karfi, da mulukiya, wanda ko shakka babu salo ne na diflomasiyyar danniya.  (Saminu)