logo

HAUSA

An shigar da Quanzhou na Sin a jerin sunayen abubuwan tarihi na duniya da aka gada daga kaka da kakanni

2021-07-25 21:03:25 CRI

An shigar da Quanzhou na Sin a jerin sunayen abubuwan tarihi na duniya da aka gada daga kaka da kakanni_fororder_quanzhou-1

A yau ne, aka zartas da bukatar shigar da Quanzhou wato cibiyar cinikayya ta teku ta duniya ta daular Song da Yuan ta kasar Sin cikin jerin sunayen abubuwan tarihi na duniya da aka gada daga kaka da kakanni a gun taron kwamitin kula da abubuwan tarihi na duniya da aka gada daga kaka da kakanni karo na 44 na hukumar kula da ilmin kimiyya da fasaha da al’adu ta MDD, UNESCO, don haka birnin Quanzhou na kasar Sin ya cimma nasarar shiga jerin sunayen abubuwan tarihi, sai dai yawan abubuwan tarihi na Sin da suka shiga jerin sunayen ya kai 56.

Bisa kudurin da aka tsara a gun taron, an ce, Quanzhou wato cibiyar cinikayya ta kan teku ta duniya a daular Song da Yuan ta kasar Sin ya shaida tsarin birni dake mashigar teku na musamman a lokacin musamman a tarihi, wanda ya hada da fannoni 22 kamar su tsarin zamantakewar al’umma, da tsarin siyasa, da sufuri, da samar da kayayyaki, da cinikayya da sauransu, wadanda suka sa kaimi ga raya birnin da samun babban ci gaba a karni na 10 zuwa 14, da kasancewa muhimmin birnin mashigar teku dake hada yankin gabashin Asiya da yankin kudu maso gabashin Asiya a kan teku, tare da samar da babbar gudummawa wajen bunkasa tattalin arziki da al’adu a wadannan yankunan biyu. (Zainab)