logo

HAUSA

Mahalarta gasar wasannin Olympics ta Tokyo fiye da 120 sun kamu da cutar COVID-19

2021-07-25 16:29:59 CRI

Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Japan suka bayar, an ce, kwamitin kula da gasar wasannin Olympics ta Tokyo ya tabbatar a taron manema labaru da aka gudanar a jiya cewa, karin mutane 17 dake halartar gasar wasannin Olympics ta Tokyo sun kamu da cutar COVID-19, ciki har da wani dan wasa dake zaune a kauyen wasannin Olympics wanda ya shiga kasar Japan daga ketare.

Bisa kididdigar da kwamitin ya gabatar a safiyar jiya, an ce, tun daga ranar 1 ga wannan wata, mutane 123 dake halartar gasar wasannin Olympics ta Tokyo sun kamu da cutar COVID-19.

Amma akwai wani labarin da aka bayar a daren jiya cewa, an sabunta yawan wadanda suka kamu da cutar zuwa 127. Sabbin mutane 4 mai yiwuwa ‘yan sanda ne dake aikin kiyaye tsaro a dakunan wasanni na Tokyo.

Banda wannan kuma, bisa ka’idar magance yaduwar cutar COVID-19 a yayin gasar wasannin Olympics ta Tokyo, ya kamata a yi bincike kan dukkan ‘yan wasa masu halartar gasar don tantance ko sun kamu da cutar ko a’a a kowace rana. (Zainab)