logo

HAUSA

Ana samun karuwar bukatar kwararrun sana’o’i a kasar Sin

2021-07-25 17:10:48 CRI

Alkaluman da hukumomin gwamnatin kasar Sin suka fitar game da bukatun guraben ayyukan da ake da su sun nuna cewa, an samu karancin kwararrun sana’o’in da ake da bukatarsu a kasar Sin a rubu’i na biyu na wannan shekarar.

Kusan rabin sabbin sana’o’i ne daga cikin 100 da ake matukar bukata a rubu’i na biyu na bana suna shafar fannonin manhajoji, da kere-kere, da fasahar sadarwa ta zamani, kamar yadda hukumar samar da ma’aikata da kyautata rayuwar al’umma ta kasar ta bayyana cikin alkalumanta na rubu’in shekara.

Binciken da aka gudanar a tsakanin bangarori ayyuka 10 da aka fi bukatarsu a rubu’i na biyu na bana ya nuna cewa, an samu karuwar karancin kwararrun injiniyoyin masana’antu, da injiniyoyin fannin sadarwa, da kwararrun injiniyoyin na’urori masu sarrafa kansu, kamar yadda alkaluman suka nuna.

Sa’an nan bangaren ayyukan hidimomi su ma akwai matukar bukatarsu, sai kuma wakilan fannin saye da sayarwa, da masu kula da gidajen abinci, da masu samar da tsaro, da masu tsabtace wurare, da kuma kwararrun masu tallata hajoji duka suna daga cikin jerin wadanda ake bukatarsu.

An gudanar da wannan kididdigar ne bisa alkaluman da aka tattara daga hukumomin hidima wajen samar da ayyuka ga jama’a kimanin 102 dake kasar Sin.(Ahmad)