logo

HAUSA

Wang Yi ya yi shawarwari tare da takwaran aikinsa na kasar Pakistan

2021-07-25 16:35:52 CRI

Wang Yi ya yi shawarwari tare da takwaran aikinsa na kasar Pakistan_fororder_dd1487b9b5dd2c64741d85771738b8c5

Memban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya yi shawarwari a tsakanin ministocin harkokin wajen Sin da Pakistan karo na 3 tare da takwaran aikinsa na kasar Pakistan Shah Mahmood Qureshi a birnin Chengdu dake lardin Sichuan na kasar Sin a jiya.

A yayin tattaunawar, Wang Yi ya bayyana cewa, Sin da Pakistan suna da kyakkyawar alakar makwabta da kuma ‘yan uwantaka a tsakaninsu, suna sada zumunci mai zurfi. Sin ta yabawa Pakistan domin nuna goyon baya ga Sin kan manyan batutuwan dake shafar moriyar kasar Sin. Sin ta nuna goyon baya ga tabbatar da ikon mallakar kasar Pakistan, da tsaron kasar, da kuma moriyar bunkasuwar kasar. Kana Sin ta goyi bayan Pakistan wajen neman hanyar samun ci gaba mafi dacewa da yanayin kasar, tare da fatan Pakistan za ta kara taka muhimmiyar rawa a harkokin yankuna da na kasa da kasa.

A nasa bangaren, Qureshi ya bayyana cewa, Pakistan tana Allah wadai da kowane irin batu dake shafar zargi kan kasar Sin ba tare da tushe ba. Pakistan ta nuna goyon baya ga matsayin Sin kan batun neman asalin kwayoyin cutar COVID-19. Kana dukkan jama’ar kasar Pakistan sun nuna goyon baya ga huldar tattalin arziki a tsakanin Pakistan da Sin, tare da fatan za a inganta tsarin yadda ya kamata. Pakistan tana son kara yin hadin gwiwa tare da Sin don sa kaimi ga shimfida zaman lafiya a kasar Afghanistan cikin lumana. (Zainab)