logo

HAUSA

An bude wasannin Olympic karo na 32 a Tokyo bayan jinkirin shekara 1

2021-07-24 15:21:20 CRI

An bude wasannin Olympic karo na 32 a Tokyo bayan jinkirin shekara 1_fororder_d844c049804846a7b73e3f487499946d

Bayan jinkirin shekara 1 saboda barkewar annobar COVID-19, an bude wasannin Olympic na lokacin rani karo na 32 a birnin Tokyo a jiya da dare.

Kimanin mutane 950, ciki har da jami’ai da ‘yan jarida ne aka bari suka shiga wajen bikin bude wasannin mai daukar mutane 68,000.

A cewar shugaban kwamitin wasannin Olympic na duniya IOC Thomas Bach, wannan lokaci ne na kyakkyawar fata, yana mai kira da a ba wasannin goyon baya.

Ya ce ‘yan wasan na aikewa da wani sakon kwarin gwiwa ga duniyar dake cikin wani muhimmin yanayi. Ya ce bikin budewar na bayyana sakon wasannin Olympic na juriya da hadin gwiwa da hadin kan dukkan bil Adama wajen shawo kan annobar COVID-19. Yana mai cewa wasannin na Olympic, wani haske ne bayan duhu.

Wasannin Olympic na Tokyo na bana ya ja hankalin ‘yan wasa 11,000 daga tawagogi 205 da kungiyar wasannin Olympic ta ‘yan gudun hijira.

Kasar Sin ta tura tawaga mai kunshe da mambobi 777 zuwa Tokyo, wadda ita ce mafi yawa da ta taba turawa ketare domin wasanni. ‘Yan wasan kasar Sin 431 ciki har da zakarun wasannin Olympic 24, za su fafata cikin wasanni 30 daga cikin 33 da za a yi a birnin Tokyo. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha