logo

HAUSA

Amurka: yawan masu kamuwa da COVID-19 yana karuwa a yawancin wuraren kasar

2021-07-24 17:03:13 CRI

Amurka: yawan masu kamuwa da COVID-19 yana karuwa a yawancin wuraren kasar_fororder_美国疫情

Rahoton mako-mako da cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Amurka CDC ta fitar jiya dangane da yadda ake fama da cutar annobar numfashi ta COVID-19 a kasar, ya nuna cewa, yanzu haka yawan masu kamuwa da cutar na karuwa a sassan kasar da yawansu ya kai kusan kaso 90 cikin 100.

Alkalumn hukumar CDC sun nuna cewa, ya zuwa ranar 21 ga wata, matsakaicin yawan masu kamuwa da cutar COVID-19 a kowace rana cikin ko wanne kwanaki 7 ya kai kimanin dubu 40 a Amurka, wanda ya karu da kaso 46.7 cikin 100 bisa na makon da ya gabata, yayin da matsakaicin yawan matattu sakamakon kamuwa da cutar a kowace rana cikin ko wanne kwanaki 7 ya kai kimanin 220 a kasar, wanda ya karu da kaso 9.3 cikin 100.

Ban da haka kuma, hukumar ta CDC ta yi bayanin cewa, karuwar adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 da matattu da kuma mutanen da suke kwanciya a asibiti sakamakon kamuwa da cutar tana da nasaba da saurin yaduwar kwayar cutar COVID-19 mai nau’in Delta, wadda ke kama mutane masu dimbin yawa cikin saurin gaske. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan